Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Jaridar New York Times ta nakalto wani jami'in sojin Amurka inda ta bayar da rahoton cewa sakamakon hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuki da Iran ta kai a baya-bayan nan kan wuraren da Amurka ke da su a Jordan da wasu kasashe da dama a yankin, sojojin Amurka 12 sun sami munanan raunuka har ta kai ga an kai su wani asibiti a Jamus domin neman jinya.
Wannan jaridar Amurka, tana nuni da ƙarfin Iran na kai hari kan wuraren Amurka, ta ci gaba da cewa hare-haren Iran a kan sansanonin Amurka 9 a duk faɗin yammacin Asiya a cikin makonni biyu bayan rushewar tsagaita wuta, suna nuna cewa ƙasar har yanzu tana da ikon yin barna ga takamaiman wuraren Amurka wanda wannan yana faruwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Trump ta sha yin iƙirarin cewa an raunana ko kuma an lalatar da ƙarfin sojin Iran gaba ɗaya.
.....
Ra'ayinka